Connect with us

Uncategorized

Ku tuna da ranar Karshe, Inji Tsoho mai shekaru 81 da aka kulle bayan da aka sace Shanayan su

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Iyalin wasu Fulani da ke zama a kauyan Kaban ta karamar hukumar Igabi a nan Jihar Kaduna, sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna a jagorancin Gwamna Nasir El-Rufai da Kwamishanan Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar da taimaka masu wajen ganin cewa an mayar masu da shanayan su guda 31 da suka bata a Ofishin ‘yan sandan yankin.

Mutanen sun bayyana da cewa shanayan su ya bata ne a ofishin ‘yan sandan bayan ‘yan kwanaki da ‘yan sanda suka fada wa gidan su da kwashe masu shanaye da tumaki akan wata zargi da ake da daya daga cikin su na cewar an gane shi da wata Bindiga, wanda ya nuna da cewa watakila yana cikin ‘yan ta’addan Jihar.

A ranar Litini, 22 ga watan Afrilu 2019 da ta gabata, missalin karfe Goma Shabiyu na tsakar rana (12PM), Hukumar tsaron Jihar Kaduna da suka kame Mallam Ibrahim sun sake shi bayan da yayi kwanaki biyar a kulle Ofishin Jami’an tsaro da ke ta Ofishin Metro, a Kaduna.

Bisa ganewar Naija News Hausa, an kame Ibrahim ne bayan da ci dage da cewa tabbas sai hukumar tsaron sun mayar masu da shanayen su da ya bata a Ofishin su kwanakin baya.

Ibrahim a bayanin shi bayan da aka sake shi, ya ce “Duk wannan tsanantawa da suke mana ba don komai bane, don shanayan mu da suka bata a Ofishin su ne. Sun Zargi yaro na da zaman dan ta’adda, amma ni dai na san Allah na kallo, kuma akwai ranar karshe.” inji shi.

“Abu daya da zan fada itace, Shanayen nan 31 nawa ne. Kuma na ci gadon su ne shekaru da yawa da suka gabata daga Iyaye na. Zan kuma ci gaba da kuzarin ganin cewa na samu sake ganin su, ko tayaya, ko da zai dauke ni tsawon lokatai ne.”

Ibrahim ya kuma sake rokon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da taimaka masa da ganin cewa an kwato masa yancin sa daga Ofishin Jami’an Tsaron Jihar.

“Shanayan nan ne kawai gado na, da su kuma nike ciyar da Iyalai na.” inji shi.