Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 22 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 22 ga Watan Mayu, 2019

1. Shugaba Buhari ya sauya daga Saudi Arabia zuwa Najeriya

Naija News ta fahimta cewa shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata, ya bar mazaunin Sarki Abdul’aziz, Sarkin Saudi Arabia don dawo wa kasar Najeriya.

Daman shugaban zai dawo kasar ne bayan gama hidimar Umrah a Makkah.

2. Ihedioha na zargin Okorocha da kin bada kudi don hidiar Rantsarwa

Sabon Gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, na zargin tsohon Gwamnan Jihar, Rochas Okorocha, da kin sake kuɗi don yin bikin rantsarwa ta ranar 29 ga Mayu.

Ihedioha da ya lashe zaben kujerar Gwamnan Jihar Imo daga Jam’iyyar PDP, ya sanar ta bakin sakataren hidimar rantsar da shi, Ray Emeana, cewa Okorocha ya ki bada kudade ga kadamar da hidimar rantsar da shi.

3. Dalilin da ya sa bai dace ga Lai Mohammed da Buhari ba da harin Obasanjo – Fani-Kayode

Tsohon Ministan Harkokin Waje, Femi Fani-Kayode ya bayyana cewa, ya kamata ne Lai Mohammed da Shugaba Muhammadu Buhari su zama na karshe ga iya daukan matakin harin tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo kan zancen Boko Haram.

Jigon a Jam’iyyar PDP ya ce, “bai dace a bakin Ministan Harkokin Sadarwa da Al’adar kasa, Lai Mohammed da kalubalantar wani ko kafa baki ga zancen Boko Haram ba.

4. Atiku zai lashe zaben Kotun Koli na Shugaban kasa – PDP

Jam’iyyar PDP a ranar Litinin, 20 ga Mayu, sun sake buga gaba da bada gaskiya da cewa dan takarar shugaban kasa na shekarar 2019 a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubabar zai ci nasara ga karar shugabanci kasar Najeriya da ake a Kotun Zabe.

Jam’iyyar adawan sun yi kira ga kwamitin karar da tabbatar da cewa an gudanar da karar a yadda ta dace da kuma adalci.

5. Gwamnatin Tarayya na zancen ƙarshe banbancewa tsakanin BSc/HND

A karshe Gwamnatin tarayya ta kafa baki ga ƙarshe banbacewar da ake tun shekarun baya tsakanin Tsarin digiri na ‘yan Makarantar Fasaha (HND) da ƙwararren digiri na BSc a kasar.

Naija News Hausa ta gane da cewa Majalisar wakilai a ranar Talata da ta gabata, ta wallafa bil na kafa dokar da za ta kawar da banbancewa tsakanin ɗalibai biyu na kwalejojin Najeriya.

6. Kotun Koli ta Tarayya ta dakatar da gwajin Fayose har zuwa 10 ga Yuni

Kotun Koli ta Tarayya ta gabatar da daga ranar gurfanar da Gwamna Ayodele Fayose zuwa ranar Jumma’a, 10 ga watan Mayu, a Kotun Tarayyar ta Legas.

An gabatar da hakan ne daga bakin Alkalin da ke jagoran karar, Mojisola Olatoregun.

7. Boko Haram: Shugabancin kasa na barazanar cewa dole sai Obasanjo ya nemi gafara daga ‘yan Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo, da kokarin tayar da tanzoma a kasar a kan zancen da yayi na ‘yan kungiyar Boko Haram da kungiyar ISWAP, da cewa wannan zancen bai dace daga wanda ake gani a matsayin dattijo.

A wata sanarwa da aka bayar ranar Talata da ta wuce a birnin Abuja, Ministan Sadarwa da Al’ada, Alhaji Lai Mohammed, ya ce “abin takaici ne ganin tsohon shugaban kasar da yayi kokarin kadamar da ci gaba a kasa da kuma dawowa da furcin da zai rabar da kuma jawo tashin hankali a kasar”

8. HISBAH sun kame Karuwai 21 da Fashe Kwalaban kayan Maye a Jigawa

Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Jigawa, HISBAH, a ranar Litinin ta kama mutane 21 da ake tuhuma da aikata laifuka da bai dace ba, haka kazalika suka kwashe wasu kwalabai kimanin 111 daga hannun su.

Babban kwamandan Hisba a jihar, Ibrahim Dahiru, wanda ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na NAN a Dutse, ya bayyana cewa sun kame mutanen ne a karamar hukumar Kazaure na jihar Jigawa.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya ta Yau a Shafin Hausa.NaijaNews.Com