Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 23 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 23 ga Watan Mayu, 2019
1. Alkali Bulkachuwa ta janye daga Hidimar Karar Atiku da Buhari akan shugabancin Najeriya
Babban shugaban Kotun Neman Yanci, da kuma ciyaman na rukunin Alkalai biyar da ke shari’ar zaben shugaban kasa, Zainab Bulkachuwa, ta janye kanta daga zancen karar.
Hakan ya bayyana ne ga Naija News a yayin da Alkali Bulkachuwa ta janye kanta daga hidimar zaben a ranar Laraba, 22 da watan Mayu da ya gabata.
2. PDP: Sanata Adeleke yayi karar IGP Adamu akan kame shi
Dan takaran kujerar Gwamnan Jihar Osun daga Jam’iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke da ke wakilci a gidan Majalisar Dattijai, ya gabatar da karar shugaban Jami’an tsaro, IGP Mohammed Adamu a kotu don kame shi da yayi a baya.
Naija News Hausa ta fahimta cewa Sanatan ya gabatar da karar ne a gaban Kotun Koli ta Ikirun, Jihar Osun.
3. Next Level: Shugaba Buhari ya gayawa Ministoci lokacin da zasu yi hidimar Mikarwa
Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci Ministocin da ke a rukunin shugabancin sa da ci gaba da aikin su har sai ranar Talata, 28 ga watan Mayu na gaba, ranar daya ga hidimar rantsar da shi a karo ta biyu a matsayin shugaban kasan Najeriya.
Shugaba Buhari ya bada wannan umarni ne a fadar sa ranar Laraba, 22 ga watan Mayu da ta wuce, bayan dawowar sa daga kasar Saudi Arabia.
4. Shugabanci: Buhari ya bada umarni a kawar da Manyan Motoci da ke kan gadar Apapa ta Legas
Shugaba Muhamadu Buhari da shugabancin kasar Najeriya ta bada umarnin cewa a kawar da Manyan Motoci da duk katangewar hanya da ke a kan gadar Apapa ta Jihar Legas, a cikin mako biyu kawai.
An sanar da hakan ne a wata sanarwa da aka bayar daga bakin Mista Laolu Akande, sakataren yadarwa ga mataimakin shugaban kasa.
5. Kotu ta gabatar da ranar da za a yi gwajin Allison Madueke
Babban Kotun Koli ta birnin Tarayyar kasar Najeriya (FCT) Abuja, ta gabatar da ranar 3 ga watan Aktoba don ci gaba da gwajin tsohon Ministan Kamfanin Man Fetur, Deziani Alison-Madueke, akan wasu zargi biyar da ke a kanta.
Kotun ta bayyana hakan ne a ranar Laraba, 22 ga watan Mayu da ta wuce.
6. An saki Ofisishin Hukumar FRSC da ake sace
Naija News Hausa ta samu tabbaci da cewa an saki Ofisoshi biyu na Hukumar Kulawa da Tafiye-Tafiyen Motoci da Babura (FRSC) da aka sace a baya.
Manema labarai sun sanar a ranar Lahadi da ta gabata cewa ‘yan hari da makami sun sace Ofisoshi biyu, Mista Abioye da Mista Bayegunni a babban hanyar Ilesha zuwa Akure.
7. Atiku ya yi karar Ma’aikaci ga shugaba Buhari a Kotu akan wata zance
Tsohon Mataimakin shugaban kasan Najeriya da kuma dan takaran shugaban kasan Najeriya ga zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar ta gabatar da karar Lauretta Onochie, akan bata masa suna da ta yi.
Hakan ya bayyana ne ranar Talata da ta wuce, daga bakin Mista Mike Ozekhome, mai bada shawarwari ga Atiku Abubakar, da cewa tsawon awowi 48 da aka bayar da Lauretta ya kare.
8. Shugaba Buhari ya jagoranci zaman tattaunawar Kwamitin Dattijan Najeriya
A ranar Laraba, 22 ga watan Mayu da ya wuce, shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci wata zaman bankwana da Kungiyar Manyan Dattijan Najeriya a fadar sa ta birnin Abuja.
Naija News ta fahimta cewa zaman tattaunawar ya fara ne a isowar shugaban, a missalin karfe 11:03 na safiyar ranar Labara.
Ka samu kari da cikakken Labaran kasar Najeriya a Shafin Hausa.NaijaNews.Com