Connect with us

Uncategorized

Kotu ta gabatar da Kame Tsohon Gwamnan Neja, Talba da kuma Gado Nasko

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Jihar Neja

Kotun Koli ta Tarayya da ke a garin Minna, babban birnin Jihar Neja, ta gabatar da bukatan kame tsohon Gwamnan Jihar, Babangida Aliyu (Talban) da kuma dan takaran kujerar Gwamna daga Jam’iyyar PDP a zaben 2019, Umar Gado Nasko.

Ka tuna cewa a da Kotu ta bada daman belin tsohon Gwamnan akan wata laifin cin hanci da rashawa da aka gane da shi.

Alkalin Kotun Kolin, Justice Aliyu, ya gabatar da janye belin da daman aka bayar ga Talba da kuma Nasko, da cewa sun nuna reni ga Kotun don kaurace wa kirar da kotun ta yi garesu don neman bayani daga bakin su.

Hukumar Kare Tattalin Arziƙi da Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Najeriya (EFCC) na zargi da karar su biyun, akan wata bincike da ganewa da aka yi na kadamar da halin cin hanci da rashawa na kudi kimanin naira Biliyan Biyu (N2 billion).

Alkalin ya kuma daga gabatar da karar zuwa ranar 27 ga watan Mayu 2019.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Rukunin ‘Yan Sandan Operation Puff Adder sun kame ‘yan Hari da Makami 15 a Jihar Sokoto.

Kwamishinan’ yan sandan jihar Sokoto, Ibrahim Ka’oje, a yayin da ake gabatar da ‘yan hari da bindigar a hedkwatar ‘yan sandan Jihar Sokoto, ya bayyana cewa lallai an ci nasara da kame ‘yan harin ne da hadin gwiwar hukumomin tsaron Jihar duka a karshen makon da ta gabata.