Connect with us

Uncategorized

Gwamnan Zamfara ya bada Naira Miliyan N83m don sayan Shanayan Sallar Eid El-Fitr

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahoto da tabbacin cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Gwamna Bello Matawallen-Maradun ya bada kudi naira Miliyan Tamanin da Takwas (N83,000,000) don sayan shanaye 750 ga hidimar Sallar Eid-El-Fitr a Arewacin kasar Najeriya.

Bisa bayanin Mista Idris Yusuf Gusau, Daraktan Sadarwa ga Jihar ya bayyana cewa shanaye 750 da za a saya din za a rabar da su ne ga ragaggagu, gwamraye, yara marasa iyaye da ke a Jihar, don taimaka masu a wannan lokacin lokacin hidimar Sallah.

Haka kuma Gwamnan, Matawallen-Maradun ya gargadi al’ummar jihar da yin amfani da wannan lokacin azumin Ramadan da kuma hidimar Sallar Eid-El-Fitr da ke gaba don neman fuskar Allah ga kwanciyar hankali, zamantakewa da ci gaba a Jihar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya sanar da cewa jihar zata fara tsarafa manja a Zamfara.

“Za mu hada hannu tare da abokan kasashen waje don gabatar da itatuwan kwakwa don tsarafa manja a jihar” inji Matawallen-Maradun.

Ya kara da cewa jihar zata sake farfado da aikin noma don inganta shi hakan a Zamfara.