Connect with us

Labaran Najeriya

Buhari/Atiku: Kalli Alkali da zai maye gurbin Bulkachuwa a Karar neman Yancin Zabe

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kotun Neman Yancin Zabe da ke jagorancin karar Shugaba Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa ta shekarar 2019, ta gabatar da sabon alkali da zai wakilci shari’ar zaben watan Fabrairu 2019.

Ka tuna mun sanar a Naija News Hausa a baya cewa Jam’iyyar adawa, PDP sun bayyana rashin amincewarsu da kasancewar Alkali Zainab Bulkachuwa a hidimar karar shugaban kasa, da zargin cewa tana da alaka da Jam’iyyar APC.

A yau Litini, 10 ga watan Yuni, Alkali M. L Garba, da zai maye gurbin Bulkachuwa a hidimar karar ya bayyana a karo ta farko a gaban kotun neman yanci.

Ka tuna da cewa bayan jayayya da cece-kuce akan rashin amincewa da Bulkachuwa, Alkalin ta gabatar da janye daga hidimar karar a ranar 22 ga watan Mayu 2019.

KARANTA WANNAN KUMA; Ko da APC ta hana, sai na fita takaran kujerar mataimakin shugaban Sanatoci – Kalu