Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari da Makami sun kashe Mutane Hudu a wata Sabuwar Hari a Jihar Katsina

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu ‘yan bindiga da ba a san da su ba a yammacin ranar Lahadi da ta gabata sun kashe mutane hudu a kauyen Tsayu a karamar hukumar Jibiya na jihar Katsina.

Naija News Hausa ta samu tabbacin hakan ne bisa rahoton da Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, ASP Anaz Gezawa ya bayar don tabbatar da al’amarin a yau ranar Litinin.

ASP Anaz ya bukaci mazauna yankin da su yi hada kai da fadakar da jami’an tsaro don kokarin kawar da ‘yan fashi da sauran muggan laifuka a jihar. An bayar da rahoton cewa mazaunan kauyan sun taru suka bi sawun ‘yan fashin, suka bi su zuwa dajin tare da nufin dawo wa da shanayen da aka sata.

A garin hakan ne ‘yan fashin suka hari mazaunan kauyan, inda suka kashe hudu daga cikin su a nan take, suka kuwa gudu zuwa cikin duhun dajin.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, a cikin wata sanarwa da ke tabbatar da faruwar lamarin, ya ce;

“DPO Jibiya ya bayyana da cewa a ranar Lahadi, 18 ga watan Agusta 2019 a misalin karfe Uku na safiya, wasu gungun ‘yan hari da bindiga sun mamaye kauyen Tsayu ta karamar hukumar Jibiya, suka kuwa kwace shanu hudu (4). Mazauna kauyan sun bi barayin da zaton ribato shanayen su, amma abin kaito a garin hakan aka kashe hudu daga cikin ‘yan kauyan” inji shi.

Shugaban ya kuwa shawarci mutanen yankin duka da su rinka daukar matakan hadin kai da hukumomin tsaro dangane da magance matsalar satar shanu, satar mutane, garkuwa da mutane, fashi da makami da kuma duk wasu masu aikata mumunar laifuka a cikin yankin.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa; Rundunar Tsaron ‘yan sanda ta Jihar Neja ta kama wani mutumi da laifin lalata da Almajirai 32 a wata makarantar Almajirai da ke a Kontagora, wata karamar hukuma a jihar Neja.