APC/PDP: Karin Labarai daga Hukuncin Kotu ta Karshe Kan Zaben Shugaban Kasa ta 2019

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Kotun daukaka da sauraron karar zaben shugaban kasa da ke a birnin Tarayya, Abuja, a yau Laraba, 11 ga watan Satumba zata dauki mataki da gabatar da hukuncin karshe kan karar da dan takaran kujerar shugaban kasa ga zaben 2019 daga Jam’iyyar PDP, babban Jam’iyyar Adawar kasa, Atiku Abubakar, ya gabatar kan rashin amincewa da nasarar shugaba Muhammadu Buhari.

A yayin da ake sauraro da gabatar da hujjoji a kotu a yau, kotun tayi Watsi a haka da Kararraki biyu da dan Atiku da Jam’iyyar PDP suka gabatar.

Kotun tayi rashin amincewa da watsi da zargin da PDP ke yi kan Takardan WAEC ta shugaba Muhammadu Buhari, da kuma dage da cewa Buhari ya cika da takara.

Ka zagaya layin Hausa.NaijaNews.Com jin kadan da samun karin bayani game da hukuncin Kotun.