Connect with us

Uncategorized

‘Yan Najeriya Zasu Bada N3,000 Don Sabunta katin zama dan kasa, N5,000 Domin Musanya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Jagorancin Katin Zama Dan Kasa (NIMC) ta ce ‘yan Najeriya za su biya N3,000 ga Remita, hanyar yanar gizo, don sabunta katunan zama dan kasa, da kuma biyan dubu biyar (5,000) don musanya katin.

Naija News ta samu tabbacin sanarwan ne kamar yadda hukumar ta fitar da jerin sakonnin ta shafin twitter (@nimc_ng) a ranar Talata.

Hukumar NIMC ta sanar cewa duk wanda ke bukatar munsayar katin zaman dan kasar ya ziyarci Ofishinsu da ke a kusa da shi don cinma hakar, amma da takardun shaidar cewa lallai shi ne ke da katin tun a farko.

A cikin takardun shaidar, “duk mai muradin sabunta ko musanya katin zaman kasar zai tafi Ofishin NIMC da takardar nuna shaidar biyan kudi dangane da hakan, kamar yadda aka sanar a sama a hanyar Remita, ta Banki, da kuma takarda da aka bashi a yayin yin rajista (NIN Slip) na NIMC.”

“Gurinmu da wannan shiri itace don tabbatar da cewa duk dan Najeriya ya yi rajistan zama dan kasa da kuma karban lambar NIN tashi, wannan kwarai da gaske ya na da muhimanci a gareshi da kasar” inji sanarwan hukumar.

KARANTA WANNAN KUMA; EFCC sun Taras da Miliyan N65,548m a Ofishin INEC ta Jihar Zamfara