Uncategorized
‘Yan Hari sun kashe Dan Sanda guda da kuma sace biyar a Jihar Zamfara
Naija News Hausa ta samu rahoto da cewa ‘yan hari da makami sun hari wasu ‘yan sanda shidda a Jihar Zamfara, sun kashe daya daga cikin su, suka kuma sace sauran.
Abin ya faru ne a karamar hukumar Anka ta Jihar Zamfara kamar yadda aka bayar ga manema labarai.
Salisu Lawali, wani mazaunin shiyar, ya bayyana ga manema labarai da cewa ‘yan hari da bindigar sun hari kauyan Sunke ne da ke karamar hukumar Anka, inda suka fada wa ‘yan sandan a yayin da suke kan aikin su. “Sun kashe daya daga cikin ‘yan sandan anan take, sun kuma sace sauran ‘yan sanda biyar din” inji Salisu.
Salisu ya kara da cewa ‘yan harin sun saki ‘yan sandan a rana ta biyu, amma ba tare da bindigar su ba.
“Ban yi tsanmanin anyi wata jayayya ko gwagwarmaya da ‘yan harin ba. Kawai dai bayan abin da ya faru ranar ta farko, kwaram ne mun gano sauran ‘yan sanda biyar din rana ta biyu an sake su ba tare da wata rauni ba, sai dai ‘yan sandan sun ce ‘yan harin sun kwace masu bindigogin su” inji Malam Salisu.
A bayanin Ciyaman na Karamar hukumar Anka, Malam Mustapha Gado, ya bayyana da cewa an kai ‘yan sandan ne don tsaro a wajen da ake tsarrafa ayuka.
Babban shugaban Jami’an tsaron yankin ya kara da cewa lallai an saki ‘yan sandan amma bindigogin su na hannun ‘yan harin.
“Mun umurci ma’aikatan wajen da dakatar da ayukan su, har sai mun kai ga hasken lamarin” inji shi.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Jami’an ‘yan sanda sun kulle Ofisoshin tsaro da suka kashe wani Ofisan Civil Defence (Hukumar tsaro da Yaki da Yancin Al’umma).