Connect with us

Labaran Nishadi

Mun taya ka Murna; Wamako da Ahmed sun aika wa Tambuwal sako bayan lashe zabe

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Bayan Hidimar zaben Kujerar Gwamna da aka gudanar a ranar Asabar 23 ga watan Maris 2019 da ta gabata a Jihar Sokoto, dan takaran kujerar gwamnan Jihar, daga Jam’iyyar APC, Ahmed Aliyu, da Sanata Aliyu Wamakko sun aika sakon nasara da kuma murna ga mai nasara ga tseren takaran kujerar gwamnan Sokoto daga Jam’iyyar PDP, Gwamna Aminu Tambuwal, kamar yadda hukumar INEC ta gabatar da hakan.

Naija News Hausa ta gane da cewa Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) ta gabatar da Tambuwal a matsayin mai nasara ga tseren takaran Gwamnan Jihar Sokoto, bayan kamala kirgan sakamakon zaben da kuma gane da cewa Tambuwal ya fiye dan adawan sa da yawar kuri’u 342.

Dan takaran kujerar Gwamnan daga Jam’iyyar APC, Ahmed Aliyu da Sanata Aliyu Wamako sun taya Tambuwal murnan lashe zaben ne a layin yanar gizon nishadi ta Twitter da gidan Gwamnatin Jihar Sokoto ke amfani da ita.

Naija News Hausa na da sanin cewa daman Aliyu mataimaki ne ga Tambuwal kamin Aminu Tambuwal ya janye daga jam’iyyar APC zuwa PDP don fitar takara.

Shi kuma Wamakko ne tsohon Gwamnan Jihar, kamin ya sauka sa’anan Tambuwal ya hau kan shugabancin Jihar Sokoto tun daga shekarar 2015.