Connect with us

Uncategorized

Diyar A. A. Kure, Tsohon Gwamnan Neja ta Mutu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Mutuwar Fatima Abubakar Kure

Mai rana ya dauki abinsa! Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Abdulkadir Kure ya rasa diyar shi na farko.

Naija News Hausa ta karbi rahoto da safen nan da cewa Fatima Abubakar Kure, diyar Tsohon Gwamnan Jihar Neja ta Mutu a birnin Abuja, babban birnin Tarayyar kasar Najeriya.

Gidan labaran nan ta mu ta samu sanin cewa Fatima ta mutu ne da barin yaron ta daya da ta haifa.

Ko da shike ba a gabatar da cikakken bayani ba game da rasuwar ta, amma dai Alhaji Abubakar Sani Bello, Gwamnan da ke kan kujerar mulkin Jihar Neja, ya gabatar da gaisuwar ta’aziyya ta musanman ga Iyalan Tsohon Gwamnan.

Gwamna Bello ya yi mamaki da mutuwar Fatima, ya kuma yi addu’a da cewa Allah ya ba Fatima madawwamiyar hutawa, ya kuma sa ta ga Jannatul Firdausi.

“Allah ya sa Fatima ta huta lafiya, ya sa ta ga Jannatul Firdausi, ya kuma baiwa dukan Iyalin Kure karfin zuciya na daukan kaddarar mutuwar Fatima.” inji Gwamna Bello.

Bincike ya bayar da cewa an riga an bizine Fatima a birnin Abuja, Allah ya sa ta huta Lafiya.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Sanatan da ke Wakilcin Jihar Kogi a Gidan Majalisar Dattijai, Sanata Dino Melaye, ya rasa tsohuwar sa, Deaconess Comfort Melaye.