Uncategorized
An sanar da Ranar zaben Ciyamomi da Kansiloli a Jihar Neja (Kalli kudin Fom)
Hukumar gudanar da Zabe a Jihar Neja (NSIEC) ta sanar da lokacin da za a gudanar da zaben kananan hukumomin gwamnatin jihar.
Naija News Hausa ta sami tabbacin hakan ne a bayan wata ganawar tattaunawa da masu ruwa da tsakin Jihar suka yi a ranar Alhamis da ta gabata a Minna, babban birnin tarayyar Jihar, inda aka sanar da cewa za a gudanar da hidimar zaben hukumomin jihar ranar 31 ga watan Yuli.
Hukumar ta ce tana sane da kuma bin doka ne wanda ya bukaci a bada daman wata daya ga ‘yan takara don taimaka wa dukkan jam’iyyun siyasa da dan takara ga shirye-shiryen neman zabi.
Hukumar ta tabbatar da bayyana kudin fom na shiga takaran neman kujerar Ciyaman a naira dubu Dari kacal (N100,000), a yayin da aka kuma masu neman kujerar Kansila zasu biya kudi naira dubu (N80,000).
Ko da shike, Majalisar Dattijan Shawara ga ‘yan takara (IPAC) ta gabatar da rashin amincewa da kudaden da aka bukaci masu neman takara da biya. Sun nuna jayayya cewa yawan kudaden zai hana wasu ƙananan jam’iyyun da ‘yan takara karfin shiga tseren saboda tsadar fom din.
“Mun ki amincewa da kudaden, mun kuma yi kira ga gwamnatin jihar, NSIEC da sauran masu ruwa da tsaki don taimakawa wajen rage tsadar fom din don ba wa kananan jam’iyyun damar shiga tseren don suma su taka tasu rawargani” inji sakataren hukumar IPAC, Mohammed Bello Maikujeri.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gwamnan Jihar Kano, Gwamna Abdullahi Ganduje ya nada Ali Makoda a matsayin ‘Chief of Staff’ (Babban Jami’in Kadamar da Tsari a Jihar).
An sanar da nadin Makoda ne a wata gabatar wa da aka rattaba hannu da sanar a jagorancin babban sakataren gwamnan Jihar, Abba Anwar, a birnin Kano, ranar Alhamis, 27 ga watan Yuni 2019.