Uncategorized
PDP: Hukumar Jami’an Tsaro ta bukaci Sanata Abbo da bayyana a gaban Hukuma
Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya ta bukaci Sanatan da ake zargi da zaluncin wata Mata Aure a birnin Abuja, Sanata Elisha Abbo, mai wakilcin Arewacin Jihar Adamawa a karkashin Jam’iyyar PDP da bayyan a gaban Hukuma don amsa tanbayoyi da aka shirya domin sa.
Mun ruwaito a Naija News Hausa ‘yan sa’o’i da suka gabata da Bidiyon da kuma yadda Sanata Elisha Abbo ya kwakwada wa matan aure Mari a Abuja.
Shugaban Jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu ya bada umurnin a kama Abbo da jami’in tsaro da ke a biye da shi, ya kuma sanya Ofisoshin tsaro don bincike mai zurfi akan lamarin.
Kamar yadda Sanatan ya dage da fada, ya ce “abin ya faru ne tun ranar 11 ga watan Mayu da ta gabata, wata daya kamin aka rantsar da mu ranar 11 ga watan Yunin, 2019.”
Ko da shike Naija News Hausa ta fahimta da cewa an gabatar da karar abin da Sanatan ya aikata ne tun ranar 14 ga watan Mayu da ta wuce a Hedikwatan Jami’an Tsaro da ke a Maitama, amma ‘yan sandan sunyi watsi da zargin, da cewa sai an nemo lambar wayan Sanatan kamin su iya daukar mataki akan zargin.
‘Yan Sanda sun bayyana da cewa suna kokarin daukan mataki da ya dace akan karar, da kuma diban daukan matakin musanman ga jami’in tsaro da ke biye da Sanata, ganin irin rashin adalci da kuma sanin abin da ya dace da Jami’in tsaron ya aikatar akan lamarin.
KARANTA WANNAN KUMA; Dalilin da yasa wani ya kashe Makwabcin sa a Jihar Kwara