Connect with us

Labaran Najeriya

Yankin Kudun Jihar Kaduna za ta ba wa Muhammadu Buhari zabe kashi 90 cikin 100 – Yusuf Bala

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Ganin zaben tarayya da za a yi watan gobe ya kusanta, Mataimakin Gwamnar Jihar Kaduna, Yusuf Bala ya yi barazanar cewa yankin Kudun Jihar za ta ba wa shugaba Muhammadu Buhari kuri’a kashi 90 cikin kashi 100 ga zaben 2019 da ta gabato.

“Za mu samar da kuri’u kimanin kashi 90 bisa 100 ga zaben 2019 don ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin sa Yemi Osibanjo sun ci zaben 2019 da ke gaba” in ji fadin Yusuf Bala bayan sun gama tattaunawar kulle da suka yi na Jam’iyyar APC tare da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osibanjo a fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja a ranar Talata da ta gabata. Ya kuma bayyana irin ci gaba da kokarin da gwamnatin tarayya ta yi a kasan tsakanin shekara uku da rabi da suka hau kujerar mulki.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Gwamna Ibikunle Amosun, Gwamnan Jihar Ogun ya umurci magoya bayansa da cewa su yi kokarin jefa wa shugaba Muhammadu Buhari kuri’ar su, ya kara da cewa shugaban ya yi kokari da gaske wajen kawo cigaba ga kasar musanman ma ga Jihar Ogun.

Yusuf Bala ya ce, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osibanjo ya riga ya shiga son jama’ar kasan ganin irin manyan cigaba da ayuka mai jawo tattalin arziki ga mutanen kasar duka da shugaban ya kirkiro.

“Farfesa Yemi Osibanjo ya rigaya ya kafa so a zuciyar al’umma da irin ayukan fahimi, tallafin kudi, da bude hanyar bunkasa tattalin arzikin kasar da ya kawo wa mutane” inji Yusuf.

Muna kuma bukatar mu kasance daya daga cikin wadanda suka samar da ci gaba a wannan kasar a karkashin shugabancin shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin sa Yemi Osibanjo.

“Manoma sun karu, ‘yan kasuwa Mata da Maza ma sun karu da wannan shirin” mu ma muna son mu kasance daya daga cikin wannan nasarar ga kasan nan.

 

Karanta kuma: Zamu yi iya kokarin mu wajen bayar da kai ga komai don ganin kungiyar Biafra ta kafu – in ji shugaban IPOB, Nnamdi Kanu