Connect with us

Labaran Najeriya

APC/PDP: Ba Shugaba Buhari ke Shugabancin Najeriya ba – in ji Sanata Bukola Saraki

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Babban Shugaban Sanatocin Najeriya, Sanata Bukola Saraki, ya bayyana da cewa lallai ba shugaba Muhammadu Buhari ba ne ke shugabancin a Aso Rock.

“Masu zuba jari ga kasa sun janye wa kasuwanci da kasar Najeriya don sun gane da cewa ba Buhari ne ke shugabancin kasar ba” inji Saraki.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa, Tsohon Sakataran Yada Labarai ga Jam’iyyar APC, Bolaji Abdullahi ya gabatar ga manema ‘Yan Jaridan Vanguard da cewa ba Shugaba Muhammadu Buhari da ‘yan Najeriya suka jefa wa kuri’a ke kan mulki ba.

Abdullahi, wanda ya kasance daya daga cikin wadanda suka janye daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC ya fada wa ‘yan Najeriya da cewa su fita daga jirgin yaudarar da Buhari ya sanya, ya ce “Ba mutumin da muka zaba a shekara ta 2015 ne ke kan mulki ba.

Ku kuma tuna da cewa Shugaban Kungiyar Iyamirai (IPOB), Nnamdi Kanu ya sha ikirarin cewa an musanya Shugaba Muhammadu Buhari da wani mai suna Jibril da ga kasar Sudan. Nnamdi ya bada shaidar hakan guda shida, a baya kuma ya yi bayyani a gidan radiyon Biafra da cewa, shi fa ya tabbata da cewa Buhari bai saura cikin Aso Rock ba, kuma an rigaya an musanya shugaban.

Sanata Saraki a bayanin shi, ya ce “Masu zuba jari ga kasa sun janye wa kasuwanci da kasar Najeriya don sun gane da cewa ba Buhari ne ke shugabancin ba”

“A wata tattaunawar cin gaban kasa da aka yi, Majalisar Dinkin Duniya bayyana irin faduwar da tattalin arzikin kasar Najeriya ta yi, har ma sun bayyana da cewa Kasar Ghana ta sha gaban kasar Najeriya, kuma ta dauke sunan liki da aka saba kirar Najeriya da ita, watau, Jigon Afrika ga tattalin Arziki”.

Ya ce, ku tuna sau da dama mun gabatar da cewa akwai wata rukuni ga shugabancin Buhari.

“Sau da dama Buhari ya bayyana ta wurin ayukan sa da cewa ba shi ne ke shugabanci ba” in ji Saraki a yayin da yake bayani da Gidan Talabijin na Afrika (AIT).

“Masu zuba Jari ga kasa sun rigaya sun gane da wannan shi ya sa suka janye daga yin kasuwanci da kasar Najeriya, amma ina bada tabbaci da cewa dan takaran ta mu, Atiku Abubakar zai magance wannan”. inji shi.

 

Karanta kumaShugaban Hukumar kadamar da Zaben Kasan Najeriya (INEC), Mahmoud Yakubu ya fada da cewa hukumar ba zata juyewa amincin da take da shi ba don wata tsanani ko damuwa, akan zaben 2019 da ke gaba.