Uncategorized
Sabuwar Hari: Mahara sun kashe mutane 25 a Jihar Zamfara
Wata Muguwar farmaki da ta dauki rayukan mazauna 25 a wata yankin ta Jihar Zamfara
Mahara sun kai wata sabuwar hari a kauyuka biyu ta yankin Magaji, a Jihar Zamfara.
Rahoto ta bayar cewa akalla mutane 25 ne suka rasa rayukansu a wannan mugun hari da aka yi a ranar Laraba, bayan wata shiga da ‘yan ta’addan suka yi akan babura. sun fado wa mutanen kauyuka biyun ne ta yankin Magaji, a Jihar Zamfara.
Mazauna kauyen a ganawar su da manema labarai na Daily Trust sun bayyana ce wa, ‘yan harin sun shigo kauyen ne a kan babura suka fado wa mutane da harbi a yayin da mutanen ke girbin dankali a gonar su da ke yankin Halilu, a nan take suka kashe mutum tara 9.
Yan harin bayan da suka aikata wannan, sun kuma juyo wa yankin da maraice shiyoyin karfe 5:00 suka kara kashe mutane uku a yayin da ake shirin bizine wadanda suka kashe da safe.
Naija News ta ruwaito Jami’an Sojojin Najeriya sun kame wasu yan Mata biyu da suka yi kokarin shiga yankin Sojojin Konduga a Jihar Borno don kai masu hari
Bayan wannan suka haura wa kauyen Gidan Kaka suka kuma kashe mutum 9 a nan take. sauran mutum hudun kuma an kashe su ne a kauyen Nassarawa Godel a ganin yan Nassarawa Godel sun je su taimaka wa Gidan Halilu da aka kaiwa hari na farko. Mallam Tukur Godel ne ya bada wannan bayyani ga manema labarun Daily Trust.
Amma dai Kakakin yada sawun Yan Sanda, Muhammad Shehu ya bayyana cewa mutane biyar kawai suka mutu kuma komai ya kwanta.
Hukumar Yan Sanda ta Jihar Zamfara su haura zuwa yankin kuma sun tabbatas da wannan kashin.
“A lokacin da suka isa wurin, an gano gawawwaki biyar tare da wani mutum da ya ji rauni sosai. An kai gawarwakin asibiti dake a Birnin Magaji.
Shugaban Yan Sanda ya umurci duka jama’ar yankin su kasance da lura su kuma yi karar duk wata motsin tashin hankali da suka ji.
Karanta Kuma wasu yan Hari sun harbe Tsohon Babban Jami’in Tsaro, Alex Badeh a birnin Abuja