Connect with us

Uncategorized

Rundunar Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 58, ribato 78 a tsakanin Kaduna, Katsina da Zamfara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rundunar Sojojin Najeriya sun sanar da cin nasarar da suka yi a ranar jiya na kashe ‘yan ta’adda 58 tsakanin Jihar Kaduna, Katsina da Zamfara in da suka ribato mutane 78 da daman ‘yan ta’addan suka sace.

Sojojin sun bayar da cewa sun sha kan rukunin ‘yan ta’addan guda goma sha 18 da ke cikin dajin da taimakon Operation Sharan Daji harma sun samu ribato wasu kayar yaki daga rukunin ‘yan ta’addan.

“Sojoji Biyu da ‘yanbanga biyu ne suka mutu wajen wannan yakin”

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Mahara sun kai wata hari a kauyuka biyu ta yankin Magaji, a Jihar Zamfara kwanakin baya inda suka kashe akalla mutane 25, an bayar da cewa sun shiga kauyen ne da babura suka kuwa fada wa jama’ar wajen da harbe-harbe.

Mai yada labarai ga rundunar sojoji Operation Sharan Daji, Major Clement Abiade ya ce Sojoji takwas 8 da ‘yan banga shidda 6 suka ji rauni sakamakon wannan yakin.

“Rundunar Sojojin Operation Sharan Daji ta kafa kai ga wannan sharar wajen zamar ‘yan ta’addan ne tun 19 ga watan Janairu kuma za ta ci gaba da hakan har zuwa watan Shida ga Shekara ta 2019 hade da hadin gwuiwar hukumomin tsaron Jihohin don ganin cewa mu lallace wajen buyar su duka da kai ga karshen hare-haren da suka aiwatar wa” in ji Clement.

Yace “Mun fara samun nasara ne ga ‘yan ta’addan tun ranar 20 ga watan Janairu bayan shiga dajin, inda muka yi ganuwar wuta da harsasu da ‘yan ta’addan da har ya dauki tsawon awowi kaddan kamin suka gudu da barin wasu kayakin yakin su”.

Naija News Hausa ta sanar a jiya 23 ga Watan Janairu, 2019 da cewa Sanannen Maikudin Afrika, Alhaji Alinko Dangote ya aika da tallafin abinci na kimanin lisafin kudi na miliyan da yawa ga wadanda aka wa hari da barna a Jihar Zamfara.

Rahoto ya bayar da cewa an kame wani cikin ‘yan ta’addan da rai, an kashe 58, kuma an lallace wajen buyar su guda goma sha takwas 18, harma an ribato rayukan mutane 75 da aka sace a baya. Bincike ya nuna da cewa da dama cikin su, an kame su ne daga Jihar Zamfara.

“A halin yanzun an mayar da su ga iyalan su bayan nuna masu kulawa” in ji Major Clement.