Connect with us

Labaran Najeriya

Dan Kungiyan Asiri ne dan Sandan da aka kashe a Jihar Edo – in ji Kwamishana Hakeem

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Ga wata sabuwa: Kwamishanan Jami’an tsaron ‘yan sanda na Jihar Edo, Hakeem Odumosun ya bayar da cewa dan sandan da ‘yan hari da bindiga suka kashe a Jihar yana cikin wata kungiyar Asiri.

Kwamishanan ya bayyana da cewa, Dan Sandan da aka samu tabbacin mutuwarshi sakamakon hari da wasu ‘yan hari da bindiga suka kai masa a ranar Asabar da ta gabata a yankin Benin, Jihar Edo da cewa yana cikin Kungiyar Asiri.

Shugaban ya bayyana hakan ne ga Hukumar Manema Labaran kasar Najeriya (NAN) a kan layi da cewa harin da aka yi wa Ofisan ya dauki wasu rayuka biyu tare da shi.

An kashe Dan Sandan ne da ke da suna Oisa Ehigie a hanyar Normayo/Sakponba a nan birnin Benin.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa wasu ‘Yan Hari da Bindiga sun kame wani Dan Takaran Gidan Majalisa na Jam’iyyar APC a Jihar Edo, mai suna Michael Ohio.

“Ofisan ya mutu ne sakamakon taimakawa wajen fada da wasu ‘yan Kungiyar Asiri da ke harin nasa kungiyar Asirin” in ji Hekeem.

“Mutane ukku ne suka mutu sakamakon wannan fadar, mutane biyu daga kungiyar da kuma ofisan da aka kashe”

Kwamishanan bayyana da cewa ya ziyarci Iyalan Ofisan, kuma ya iya bayyana masu da cewa “wannan kashi na ‘yan kungiyar Asiri ne kuma shima Ofisan daya ne daga cikin kungiyar“.

Ya kara da cewa ana bincike akan wannan kashin, kuma sun iya ribato wasu makamai sakamakon binciken.

 

Karanta kuma: Shugaba Buhari ya sanya dokar ‘Rashin nuna banbanci ga Raggagu’