Labaran Najeriya
INEC: Karanta dalilin da ya sa shugaba Buhari bazai iya dakatar da Farfesa Mahmood ba
Gwagwarmaya akan zaben 2019
Bayan daga ranar zaben shugaban kasa da hukumar gudanar da zaben kasa, INEC ta yi da tsakar daren jumma’a misalin karfe 2:00 na dare, ‘yan awowi kadan da ya kamata a fara zaben 2019, fade-fade ya bi ko ta ina a yanar gizon da bukatar cewa gwamnati ta dakatar da Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben kasa.
Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da martani akan wannan bayanin, ya ce “A cikin wannan zafin lokaci da hali da ake ciki, ba zani iya dakatar da Mahmood ba” inji shi.
“Dole ne sai gidan majalisa sun bada hakan bayan tattaunawa”.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana da cewa yana da murna mara matukan gaske da irin shirye-shiryen da Hukumar gudanar da zaben kansa (INEC) ke yi don zaben 2019. Ya ce “Ina da fatan cewar Hukumar za ta tabbatar da zabe mafi kyau, da rashin makirci da tashin hankali a kasar nan, ganin irin tabbaci da shiri da shugaba hukumar Mahmood Yakubu ya gabatar wajen ganawar da muka yi na tattaunawar majalisar dokokin jiha a birnin Abuja”
Duk da hakan muna da sani a Naija News kamar yadda abin ya mamaye yanar gizo, da zargin cewa shugaba Muhammadu Buhari da kadamar da shirin tsige shugaban hukumar.
Mun kuma gane da cewa hadaddiyar hukumar kamfanonin yada labaran Najeriya ta hanyar yanar gizo (OPAN), sun bukaci gwamnatin Najeriya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da dakatar da shugaban hukumar INEC don matakin da ya dauka na daga zaben ranar Asabar da ta gabata.
Mallam Garba Shehu, Mai bada shawara ga shugaban kasa a sashin hanyoyin labarai, ya ce “Karya ne wannan zargin, shugaba Buhari bai da wata shiri na dakatar da shugaban hukumar INEC.
“Duk wannan zargin karya ce, Ba wata abu mai kama da hakan” inji shi.
“Duk mai jita-jitan cewa shugaba Muhammadu Buhari na shirin yin haka ya je ya binciki dokar kasa” inji Garba.
Ko da shike dai, hukumar INEC ta gabatar da sabuwar rana da za a fara zaben.
- Zaben shugaban kasa – Ranar Asabar, 23 ga Watan Fabrairu
- Zaben Gidan Majalisai – 9 ga Watan Maris
Wanna itacen sanarwan Farfesa Mahmood a yayin da ya ke gabatar da daga zaben Asabar da ta gabata.
Karanta wanna kuma: ‘Yan Sanda sun ci karo da Buhunan Takardun zabe 17 da aka riga aka dangwala yatsa