Connect with us

Uncategorized

Jihar Neja: Ku kwantar da hankalin ku, ba wata matsala, Abu Lolo ya gayawa bakin Jihar

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamna Abubakar Sani Bello (LOLO), Gwamnan Jihar Neja ya gayawa bakin da ke zama a Jihar da cewa su kwantar da hankalin su, da cewa ba wata matsala a garesu, musanman ga zaben gwamnoni da ta gidan majalisar Jiha da za a soma ranar Asabar ta makonnan.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Dr. Amina Abubakar Sani Bello, matan Jihar Neja ta ba wa Mata 150 tallafin kudi na #10,000 ga kowanansu a Mariga, Jihar Neja

Gwamna Bello ya gabatar ne da wannan a wata ganawa da yayi da manyan shugabannin yarurruka da ke zama a Jihar a ranar Talata, 5 ga watan Maris, 2019 da ta gabata, a babban birnin Jihar, Minna. An gudanar da zaman ne a jagorancin shugaban kungiyar, Dakta Eze Pampas.

“Gwamnatin mu za ta ci gaba da samar da zamantakewa ta kwarai ga bakin da ke zaune a Jihar mu, don gudanar da ayukan su a hanyar da ta dace” inji shi.

“Ina kara gabatarwa da cewa mun bada dama ga baki da su shigo Jihar mu don gudanar da ayukan su da sana’a’o’in  su yada suke so. Wannan ci gaba ce a garemu. Zamu kuma tabbatar da kare rayukar ku da kayakin kun duka” inji shi.

Gwamnan ya kara da fadin cewa, Jihar Neja a shugabancin sa bata taba nuna banbaci ga tsakanin Mazunin Jihar da bakin da suka zo daga wasu jihohin kasa.

“Matakin da jihar ta dauka na biyar kudin jarabawar NECO ga ‘yan makaranta sakandari an yi hakan ne kawai don bashin kudi da jihar ke ciki, amma ba don nuna banbanci ba” inji shi.

“Mun cinma bashin kudi na kimanin kudi naira miliyan N600 ga hukumar NECO, a lokacin da muka hau mulki. Amma mun samu daman biyar bashin, kawai mun rage ne da bashin naira Miliyan N250.

 

Karanta wannan kuma: An fara rajistan baji na farko (Batch A) na ‘yan bautan kasa (NYSC)