Labaran Najeriya
Kalli yadda aka marabci Shugaba Buhari da Matarsa a dawowarsu daga Daura a yau
Shugaba Muhammadu Buhari da matarsa Aisha Buhari sun komo Abuja a yau bayan ‘yan kwanaki a Daura tun kamin ranar zaben Gwamnoni da suka ziyarci Katsina don zaben. Kamar yadda muka sanar a baya a Naija News Hausa da cewa Buhari da Aisha sun ziyarci Daura gabadin zaben gwamnoni da ta gidan majalisar wakilai.
Shugaban, a yau Talata, 12 ga watan Maris 2019, shi da matarsa sun halarto Abuja daga jirgin sama, a fillin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin tarayya.
Kalli yadda aka marabci shugaba Buhari da Aisha a kasa;
Mun sanar a Naija News Hausa da safiyar nan da cewa an gabatar da Lauyan da zai jagoranci tsayawa karar zargi da Atiku Abubakar, dan takaran Jam’iyyar PDP ke yi ga shugaba Muhammadu Buhari akan zaben 2019.
Sultan na Sokoto, Sarki Muhammad Sa’ad a bayanin sa kwanakin baya wajen ziyarar shugaba Buhari, ya karfafa ‘yan Najeriya duka da daukar kaddarar ga nasarar shugaba Muhammadu Buhari ga zaben shugabanci na karo biyu a kasar.
“Na shawarci al’ummar Najeriya da daukar wannan nasara a matsayin kaddara da kuma gane da cewa wannan nufin Allah ce da ganin shugaba Buhari ya koma ga kujerar mulkin kasar Najeriya, kuma babu mai iya canza wannan” inji shi.
Karanta wannan kuma: Dan Kunar Bakin Wake ya tayar da Bam kusa da wata Ikklisiya a Jihar Adamawa