Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 26 ga Watan Maris, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 26 ga Watan Maris, 2019
1. An Mika wa shugaba Buhari Rahoton Albashin Ma’aikata
An bayar da takardan rahoto akan yadda za a samu biyan kankanin kudin albashin ma’aikatan kasa ta naira 30,000 ga shugaba Muhammadu Buhari.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu ga takardan biyan kankanin albashin ma’aikata na naira dubu talatin.
2. Mataimakin dan takaran kujerar Gwamna a Jam’iyyar AAC ya koma PDP a Jihar Rivers
Jam’iyyar PDP ta yi sabon bako a yayin da mataimakin dan takaran kujerarn Gwamna daga jam’iyyar AAC a Jihar Rivers ya janye daga jam’iyyar da komawa ga jam’iyyar PDP.
Akpo Bomba ya gabatar ne da hakan ‘yan kwanaki kadan bayan da aka kamala zaben gwamnoni a jihohin kasar.
3. Ba zamu raba shugabancin mu da PDP ba – inji Oshiomhole
Babban Ciyaman na Jam’iyyar APC ga hidimar zaben tarayya, Adams Oshiomhole ya gabatar da cewa jam’iyyar APC ba za ta rabar da kujerar shugabancin ta da jam’iyyar PDP ba a gidan Majalisar Dattijai.
Oshiomhole ya bayyana hakan ne a wata gabatarwa da yayi ga zaman tattaunawar da Jam’iyyar APC tayi da ‘yan gidan majalisa.
4. An kara daga karar El-Zakzaky zuwa gaba
Kotun Koli ta Jihar Kaduna ta daga zancen karar shugaban kungiyar ‘yan Musulumman Najeriya da aka fi sani da IMN, Ibrahim El-Zakzaky, da Matarsa, Zeenat.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa ‘yan Shi’a sun gudanar da zanga-zanga a garin Abuja don bukatar a saki shugaban su.
5. Kotu ta Janye Karar dakatar da hidimar zabe a Jihar Bauchi
Kotun Koli ta birnin Abuja tayi watsi da karar da Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abubakar da Jam’iyyar APC suka gabatar na kalubalantar hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) akan dakatar da hidimar zaben Jihar Bauchi a baya.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Kotun Koli ta birnin Abuja ta hana hukumar INEC da gudanar da hidimar zabe a Jihar Bauchi.
6. Jam’iyyar APC ta Jihar Sokoto sun yi watsi da sakamakon zaben Jihar
Jam’iyyar APC ta Jihar Sokoto sun gabatar da rashin amincewar su ga sanar da Gwamna Aminu Tambuwal, dan takaran kujerar Gwamna daga jam’iyyar PDP a matsayin mai nasara ga zaben kujerar gwamnan Jiahr ga zaben ranar Asabar da ta gabata.
Hukumar INEC ta sanar a ranar Lahadi da ta gabata da cewa Tambuwal ne ya lashe tseren takaran kujerar gwamnan Jihar, bisa yawar kuri’u fiye da dan adawan sa.
7. Kasar Turai sun kafa baki ga nasarar shugaba Muhammadu Buhari
Kungiyar Kasar Turai (EU) ta jinjina da kuma taya shugaba Muhammadu Buhari murna ga samun cin nasara ga zaben shugabancin kasar Najeriya a karo ta biyu.
Kungiyar sun gabatar ne da gaisuwar a wata wasika da aka wallafa ga shugaban da kuma aka bayar a ranar 22 ga watan Maris 2019.
8. Sanata Saraki na kokarin ya ci gaba da cin albarkacin shugabanci
Jam’iyyar APC a gidan Majalisar Dattijai na zargi da kuma jita-jitan cewa shugaban Sanatocin kasar Najeriya, Bukola Saraki na kokarin ya ci gaba da cin albarkacin shugabancin gidan majalisar bayan da ya fadi ga zabe.
Naija News Hausa na da sanin cewa Sanata Saraki ya fadi daga tseren takaran kujerar Sanata daga yankin Jihar Kwara.
Ka samu cikakken labarun kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa