Connect with us

Uncategorized

‘Yan Sanda Biyu suka Mutu a harin Kakanji ta shiyar Birnin Gwari – inji Yakubu Sabo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, ta gabatar a ranar Lahadi da ta gabata da cewa sun yi nasara da kashe ‘yan hari da makami biyu daga cikin wadanda suka aiwatar da mugun harin da aka yi a Kakanji, karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar a daren ranar Asabar da ta gabata.

Yakubu Sabo, Kakakin yada labarai ga Hukumar, ya bayyana ga Kungiyar Manema labaran Najeriya (NAN) a Jihar Kaduna da cewa lallai Jami’an tsaron ‘yan sanda biyu suka mutu sakamakon harin.

“Mun karbi wata kirar gaugawa ne daga DPO Randagi a ranar 6 ga watan Afrilu da maraice da cewa ‘yan hari da makamin sun mamaye yankin Kakangi ta karamar hukumar Birnin Gwari, wata kauye da ke kusa da Jihar Neja da harbe-harben bindiga ko ta ina” inji fadin Randagi ga Yakubu.

“A nan take Hukumomin tsaron Jihar suka hada kai da halartan wajen don ganawar wuta da mahara da bindigar na tsawon lokatai”

“Darukan tsaron mu sun samu kashe Ukku daga cikin ‘yan ta’addan bayan da sauran suka fada daji da gudu da zafin raunuka”

“Ko da shike, Biyu daga cikin Jami’an tsaron mu sun sadaukar da ransu da mutuwa a ganawar wutan” inji Sabo.

Ya ci gaba da bayyana sunan Ofisoshin da suka mutu a ganawar wutan;

  • Aliyu Mohammed
  • Rabiu Abubakar

Ya kara da cewa ‘yan sanda biyun na daga rukunin tsaron Jami’an ‘yan sandan da ke yankin Randagi ne.
Ya kuma bayyana da cewa Sajan Ibrahim Nasir tare da wasu jami’an tsaro shidda sun yi raunuka da dama, amma dai ana basu kulawa a Asibitin Janara da ke a Birnin Gwari.

Bisa bayanin Sabo, ya fada da cewa Kwamishanan Jami’an tsaron yankin ya nuna bakin ciki da harin, ya kuma bada tabbaci ga al’ummar yankin da cewa zai tabbatar da cewa hukumar tsaro ta gano wadanda suka aiwatar da harin, a kuma hukunta su a bisa dokar kasa.

Kwamishanan ya bukaci al’ummar yankin da bayar da duk wata alama ko liki da suka iya gane da ita da zai iya taimaka wa hukumomin tsaro da cin nasara wajen kame ‘yan ta’addan.

Ya kuma karshe da yi wa jami’an tsaro da suka mutu fatan Aljanna da kuma yiwa wadanda suka yi raunuka fatan samun sauki a gagauje.

Mun ruwaito a Naija News a baya da cewa wani mutumi da ake dubin shi da tabuwar kwakwalwa, ya kashe daya daga cikin Jami’an tsaron ‘Yan Sanda a Jihar Kwara da saran Adda.