Uncategorized
Kalli dalilin da ya sa aka Tsige Hakimai biyu a Jihar Katsina
Hukumar Sarakai ta Jihar Katsina sun sanar da Tsige Hakimai biyu a wata yankin Jihar.
Naija News Hausa ta gane da cewa Hukumar sun yi hakan ne da zargin cewa hakiman sun nuna halin rashin biyayya. Hukumar ta gabatar ne da hakan a ranar Talata da ta gabata, daga bakin Sakataren Kungiyar da kuma Sallama Katsina, Bello Ifo, da cewa Hukumar tayi hakan ne bisa kan kwakwarun dalilai.
Mutane biyun da aka dakatar su ne kamar haka; Alhaji Aminu Kabir Usman, Durbin Katsina, watau Hakimin yankin Jikamshi, da kuma Alhaji Abdulkarim Kabir Usman, Sarkin Sullubawan Katsina, watau hakimin yankin Kaita.
Ko da shike ba a bayyana a fili irin rashin jin da Hakiman suka yi ba, amma an gabatar da cewa sun karya dokar kungiyar ne bisa sharadu da ya gabaci tsigewar su.
Bello ya bayyana da cewa an riga an kafa wata sabuwar Kwamiti don bincike da kuma tattauna akan halin rashin biyayya da Hakiman suka yi.
Naija News Hausa ta sanar a baya da cewa Hukumar Jami’an tsaron Jihar Neja sun kame wata Macce mai shekaru 50 da haifuwa da zargin kisan Kai.
Wata Mata mai suna Hafsat Aliyu ta hada kai da yaron ta mai suna Babangida Usman, suka kuma yiwa Maigidan da ake kira Ali Haruna duuka har ga mutuwa.