Labaran Nishadi
#Ramadan: Kalli Yada ‘Yan Sanda ke Rabar da Abincin bude baki ga Direbobi a kan hanya
Naija News Hausa ta gane da hotunan wasu ‘yan Sandan kasar Qatar da ke raba wa direbobi da ke bin kan hanyar da suke tsaro abincin bude baki.
Gidan Labaran nan ta mu ta gane da hakan ne a wata sakon da wani mai likin nishadi ta @RadicalYouthMan ya aika a layin yanar gizon nishadi ta Twitter a yau.
Hotunan ta nuna wasu Jami’an tsaron ‘yan Sandan a yayin da suke rabar da abinci ga direbobi. Naija News Hausa ta gane cewa sunayin hakan ne don neman lada. Sun kuma rabas da abincin ga direbobin da ke tsare kan hanyar sakamakon dogon layi, suka basu da zuciya daya don su samu abin shanruwa.
Da ganin wannan, wani dan Najeriya ya tura sako da cewa “Wannan Dan Sandan mutum ne kamar mu ‘yan Najeriya, Jini daya ke yawo a jijiyar shi kamar yadda take a tamu jikin. Amma mu sai kirar matsala muke yi ga kanmu” inji shi.
Kalli hotunan a kasa;
https://twitter.com/RadicalYouthMan/status/1128206422322360320