Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 17 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 17 ga Watan Mayu, 2019

1. Hukumar INEC ta daga ranar zaben Gwamna ta Jihar Kogi da Bayelsa

Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasar Najeriya (INEC), ta gabatar da daga  ranar yin zaben Gwamnoni ta Jihar Kogi da Jihar Bayelsa zuwa gaba.

Naija News ta samu ganewa da hakan ne a wata sanarwa da darektan yada fasaha ga masu zabe, Mista Festus Okoye, ya bayar a ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu.

2. Shugaba Buhari ya bayar da Gurbin sa ga Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Alhamis da ta gabata ya dauki gurbin shugaba Buhari da wakilcin zaman tattaunawa da Hukumar Manyan Shugabannan Tarayyar Kasa, a birnin Abuja.

Naija News Hausa ta gane da cewa taron an fara shi ne tun ranar Laraba da ta gabata har zuwa ranar Alhamis.

3. Gidan Majalisar Dattijai ta gabatar da sabon ranar Dimokradiyyar kasar Najeriya

A ranar Alhamis da ta wuce, Majalisar Dattijai sun gabatar da sabon bil na komar da ranar 12 ga watan Yuni ta kowace shekarar a matsayin ranar Dimokradiyya.

Wannan matakin ya biyo ne bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da cewa za a musanya ranar 29 ga watan Mayu da ranar 12 ga watan Yuni, a matsayin ranar tunawa da komawar Gwamnatin farar hula.

4. EFCC ta kalubalanci Magatakardan Gidan Majalisar Dattijai

Hukumar Yaki da Kare Tattalin Arzikin kasa da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta Najeriya, sun kalubalanci, Mista Mohammed Sani-Omolori, bisa yadda ya tafiyar da asusun gidan Gidan Majalisar Dattijai.

A ganewar Naija News, Hukumar EFCC ta kwace Katin Tafiye-tafiye zuwa kasar wajen Sani don hana shi guduwa.

5. Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi kasar Saudi Arabia don Hidimar Umrah

A ranar Alhamis da ta wuce, shugaba Muhammadu Buhari ya bar kasar Najeriya zuwa ziyarar kasar Saudi Arabia don wata hidima da aka gayyace shi da kuma hidimar Umrah.

Naija News Hausa ta fahimta cewa shugaban ya tafi ne hade da wasu mabiya daga kasar Najeriya.

6. Majalisar Dattijai ta gabatar da Godwin Emefiele a matsayin Gwamnan Bankin Tarayya (CBN)

Naija News Hausa ta samu tabbacin Majalisar Dattijai da gabatar da Godwin Emefiele, a matsayin Gwamnan Bankin Tarayyar Kasar Najeriya a karo ta biyu na tsawon shekara 5.

Hakan ya bayyana ne bayan da Bukola Saraki, shugaban Sanatocin Najeriya ya rattaba hannu da gabatar da Emefiele a karo ta biyu da goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari.

7. Oshiomhole da APC ke da hakin Goyon Bayan EFCC ga neman kame ni – inji Okorocha

Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha ya zargi Ciyaman na Tarayyar Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da bada hadin kai ga Hukumar EFCC don kame shi.

Okorocha ya bayyana zargin ne a wata kara da ya wallafa, wadda ya kuma gabatar ga Kotun Koli ta birnin Abuja.

8. Gwamna Ganduje ya bayar da Miliyan N6m, kowane ga Zainab Aliyu da Ibrahim

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayar da kyautar kudi Naira Miliyan  Goma Shabiyu (N12 million), Miliyan Shidda ga Zainab Aliyu, Miliyan Shidda kuma ga Ibrahim Abubakar da aka sako daga kasar Saudi Arabia bayan kame su da aka yi a kan zargin daukar mugan kwayoyi.

Naija News Hausa ta fahimta da hakan ne bisa wata sanarwa da Gwamna Ganduje ya bayar da kansa a Jihar Kano.

Ka samu Kari da Cikakken Labaran Najeriya a Shafin Hausa.NaijaNews.Com