Labaran Najeriya
Shugaba Buhari ya nada sabon Ciyaman na Hukumar NNPC
0:00 / 0:00
A ranar Talata, 25 ga watan Yuni 2019 da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari a birnin Abuja, ya gabatar da Dakta Thomas John a matsayin sabon Ciyaman na rukunin kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC).
Naija News Hausa ta gane da hakan ne bisa wata sanarwa da Daraktan kamfanin NNPC, Dakta Maikanti Baru ya rattaba hannu a birnin Abuja ranar Talata.
Ya bayyana da cewa “Mista Thomas zai fara aiki ne a Ofishin sa a gaggauce ba tare da jinkiri ba, har sai an sanya sabon Ministan Man Fetur.”
Ka tuna mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabon Darakta na Kamfanin NNPC.
KARANTA WANNAN KUMA; Arewa Ku Manta da zancen neman Shugabanci a 2023 – inji Shehu Sani
© 2025 Naija News, a division of Polance Media Inc.