Uncategorized
Kalli Ranar da za a fara zaben Kananan Hukumomin Jihar Zamfara
Hukumar Gudanar da Zaben Jihar Zamfara (ZASIEC) ta gabatar da ranar da zasu kadamar da zaben Kansilolin Jihar Zamfara.
Shugaban Hukumar Zaben Jihar Zamfara, Alhaji Garba Muhammad ya gabatar da hakan ne a ranar Litini da ta gabata a garin Gusau da cewa hukumar zasu fara kadamar da zaben Kananan hukumomin Jihar a ranar 27 ga watan Afrilu 2019.
Naija News Hausa ta gane da cewa Jihar Zamfara na daya daga cikin Jihohin da ke fuskantar matsalar hare-hare, ta’addanci, Sace-sacen mutane da ire-iren mugayan halaye.
A halin yanzu Gwamnatin Tarayya ta samar da karin Rundunar Jami’an tsaro a Jihar don yaki da ta’addanci a Jihar.
An gabatar a baya da daga ranar da ciyamomin kananan hukumomin Jihar zasu sauka daga shugabanci. Ya kamata daman su kare shugabancin su ne tun ranar 2 ga watan Janairu, 2019 kamin aka daga ranar karewar zuwa ga ranar 2 ga watan Mayu ta shekarar 2019.
Shugaban Hukumar zaben Jihar, Muhammad ya gargadi al’uman Jihar da kuma neman hadin kai daga ‘yan ruwa da tsakin Jihar wajen don ganin cewa hidimar zaben ta kasance da kyau cikin kwanciyar hankali.
“Ina mai gabatar ga ‘yan takara da kuma Jam’iyu da fara kadamar da hidimar ralin su akan neman kujerar kansila ga kananan hukumomin su.” inji Muhammad.
Hukumar zaben Jihar ta kuma kafa wata kwamitin da zata bada ganewa da fasaha akan hidimar zaben gabadin lokacin zabe.
Ya karshe da cewa za a ci gaba da sanar da duk wata sabon mataki akan hidimar a nan gaba.