Connect with us

Uncategorized

Ta’addanci: An kafa Dokar ƙuntatawa na tsawon awowi 24 a Jihar Kaduna

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa dokar ƙuntatawa na tsawon awowi 24 a yankin karamar hukumar Kajuru.

Naija News Hausa ta gane da cewa Gwamnatin Jihar ta gabatar da dokar ne bayan wata sabuwar hari da ‘yan ta’adda suka kai a yankin.

Ko da shike ba cikakken bayanin akan yadda harin ya faru da kuma ko wace irin barna ne aka yi a yankin, amma dai Naija News ta gane da cewa Kajuru na daya daga cikin karamar hukumar Jihar Kaduna da ke fuskantar hari a kowace lokaci.

An gabatar ne da wannan dokar ƙuntatawa a yau a layin yanar gizon nishadarwa ta Facebook, kamar yadda Samuel Aruwan, Kakakin yada yawun Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya rabar.

“Bayan harin da ‘yan ta’adda suka kadamar a Kasuwan Magani a baya, Gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar da dokar ƙuntatawa ta tsawon awowi 24 a dukan kananan hukumomin Jihar, musanman karamar hukumar Kajuru. Ba za a dakatar da ƙuntatawa ba kuma sai har an bada sabuwar umarni.” inji sanarwan Aruwan.

Mun ruwaito a baya a wannan gidan yada labarai ta mu da cewa Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna sun kashe barayi ukku a Jihar a wata ganawar wuta.