Connect with us

Labaran Najeriya

Ina murna da gaske da shirin da Hukumar INEC ke yi game da zaben 2019 – Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana da cewa yana da murna mara matukan gaske da irin shirye-shiryen da Hukumar gudanar da zaben kansa (INEC) ke yi don zaben 2019 da ta gabato.

Mai bada shawarwari ta musamman ga shugaban kasa, Garba Shehu ya fada da cewa shugaba Buhari ya gabatar da wannan ne a wata zaman Tarayyar Turai (EOM) da suka yi a brinin Abuja.

Ya ce “Ina da fatan cewar Hukumar za ta tabbatar da zabe mafi kyau, da rashin makirci da tashin hankali a kasar nan, ganin irin tabbaci da shiri da shugaba hukumar Mahmood Yakubu ya gabatar wajen ganawar da muka yi na tattaunawar majalisar dokokin jiha a birnin Abuja”

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa shugaba Buhari ya gana da manyar kasar Najeriya kamar su Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan, Abdulsalami Abubakar, Gwamnonin Jiha da sauran manyan kasa a birnin Abuja ranar Talata, 22 ga watan Janairu, 2019.

“Bayan takara da na yi sau hudu a baya a kasar nan, Ina iya bada tabbacin cewa tun shekara ta 2015, Na’urar zabe ta taimaka da gaske wajen gudanar da aikin zabe a kasar na” in ji Buhari

“Shekara bisa shekara, muna samun ci gaba wajen gudanar da shirin zabe a Najeriya”

Kamar yada muka sanar a Naija News Hausa a ranar talata da ta wuce da cewa Shugaban Hukumar kadamar da Zaben Kasar Najeriya (INEC), Mahmoud Yakubu ya fada da cewa hukumar ba zata juyewa amincin da take da shi ba don wata tsanani ko damuwa.

Shugaba Buhari ya ce “Jam’iyyar APC na da shirin da manufa ta kwarai game da tsaron kasar nan, zaman lafiya, tsarafa tattalin arziki, da kuma samar da aiki ga ‘yan Najeriya har ma da yaki da cin hanci da rashawa”.

Ya karshe da nuna godiya ga manya da suka nuna kulawa da bayyana manufofin su ga zabe ta gaba da kuma ci gaban kasa Najeriya.

 

Karanta kuma: Jami’an Sojojin Ruwar ta Najeriya sun fid da Fam na shigar hukumar