Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 29 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 29 ga Watan Yuli, 2019
1. 2023: Dalilin da ya sa ya kamata Buhari ya mika mulki ga Kudu – Fasto Bakare
Babban Fasto da ki wakilcin Ikilisiyar Latter Rain Assembly, Tunde Bakare, ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da mika shugabancin kasar Najeriya ga ‘yan Kudu a shekarar 2023 da ke gabatowa.
Babban malamin ya bayyana hakan ne ga manema labaran The Sun, da cewa ba za a bar arewa kadai da ci gaba da mulkin sauran al’umma ba har abada.
2. Osinbajo ya Ziyarci Iyalin marigayi mai daraja Owolabi
A ranar Lahadi da ta gabata, Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya kai ziyara ga iyayen marigayi Precious Owolabi.
Naija News ta ruwaito a baya da cewa Owolabi, wanda ya kasance mai rahoto tare da gidan talabijin na Channels TV, ya mutu a yayin wata arangamar da ta gudana tsakanin mambobin kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) wanda kuma aka fi sani da Shi’a da kuma jami’an ‘yan sanda na Najeriya.
3. Nnamdi Kanu Ya Bayyana Wanda ya bada umarnin a tsananta masa
Shugaban kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya zargi babban jami’in Burtaniya da sanya hannu a neman kisansa.
Najia News Hausa ta fahimta da cewa Nnamdi ya bayyana hakan ne a wata rahoto da ya bayar akan Gidan Radiyon Biafra a ranar Asabar da ta gabata.
4. Dangote na shirye don zuba Jarin Biliyan N288 ga tsarafa Madara a kasar
Jagoran kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana shirin kashe dala biliyan (N288 biliyan) a harkar samar da tsarafa madara ga tsawon shekaru Uku ta gaba.
Naija News ta fahimci cewa Dangote zai mallaki shanaye 50,000 nan da shekarar 2019, sannan zai samar da lita miliyan 500 na madara a kowace shekara.
5. ‘Yan Shi’a Sun yi barazanar ci gaba da yin Zanga-zanga duk da katangewa da aka masu
Wani mai magana da yawun kungiyar Harkar Musulunci ta Najeriya (IMN) da aka fi sani da suna Shi’a, ya mayar da martani game da dokar katangewa da Gwamnatin Tarayya ta bayar game da zanga-zangar da suke yi a birnin Abuja, bisa umarnin Kotun Koli.
Naija News ta fahimci cewa Kakakin wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters sun bayyana da rashin gane da shi, ya fada da cewa duk da cewa kungiyar ba ta samu sanarwar daga kotu ba, amma ya ce zanga-zangar su zata ci gaba har sai an saki shugaban kungiyar su, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.
6. Gwamnonin Kudu Maso Gabas na taron kofa kulle
Gwamnonin da suka fito daga yankin Kudu maso Gabashin Najeriya a ranar Lahadi sun gana akan matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin.
Naija News ta samu gane da cewa taron yana gudana ne a gidan gwamnatin jihar da ke a Enugu, babban birni Jihar.
7. Sojojin Najeriya Sun Kashe Mutane 5, An Kama Wasu ‘Yan bindiga 4 A Kaduna
Runduna Sojojin Najeriya ta 1 Division sun sanar da kashe wasu ‘yan fashi biyar da kuma kame wasu mutane hudu a kananan hukumomin Chikun da Igabi ta jihar Kaduna.
Naija News ta fahimci cewa sojojin sun kama tare da kashe wasu ‘yan bindiga a wata zagaye da suka kai a yankunan da ke a cikin jihar.
8. Ka Kalubalanci jagorancin Yari, Jigon APC sun gayawa Matawalle
Wasu shugabannin da Jigo a Jam’iyyar APC ta jihar Zamfara sun yi kira ga gwamna Bello Matawalle da ya binciki gwamnatin tsohon Gwamnan Jihar, Abdulaziz Yari.
Kungiyar sun bayyana hakan ne ga Gwamnan a yayin wata zama da suka yi a Gusau a ranar Asabar din da ta gabata.
9. Ku bar ‘Yan Shi’a, Ku bi bayan makiyaya da Miyetti Allah – Ozekhome ya gayawa Buhari
Lauyan kundin tsarin mulki, Mike Ozekhome ya gargadi shugaba Muhammadu Buhari da ya tafi bayan Miyetti Allah da kuma Makiyaya Fulani da manta da zancen bin ‘yan Shi’a.
Ya furta hakan ne a lokacin da yake mayar da martani ga zancen da Gwamnatin Tarayya ke yi na batun daukar matakin musanman na dakatar da hidimar ‘yan kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) wacce kuma aka fi sani da Shi’a.
Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNewsHausa