Connect with us

Labaran Najeriya

2023: Tsohon Gwamnan Zamfara, Yarima Ya bayyana Shirin Fita Takarar Shugaban Kasa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yarima, yayin da yake magana kan shugabancin Najeriya a shekarar 2023, ya ce watakila zai iya fita takara a matsayin shugaban kasa dubin kiraye-kirayen da amintattunsa suke yi da neman ya fita takara.

Naija News Hausa ta gane da cewa Yarima ya bayyana hakan ne a Gusau, yayin wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon Najeriya, watau Pride FM, na jihar Zamfara.

Tsohon gwamnan duk da cewa a baya ya yi alkawarin ba zai taba neman kowane mukami na siyasa a jiha ba ya yi ikirarin cewa har yanzu dai yana yin la’akari da kiran da amintattun nasa ke yi na bukatarsa da ya fito takara 2023.

Yarima ya bayyana dalla-dalla yadda ya tattauna da Shugaba Muhammad Buhari game da tsohon gwamna Abdulaziz Yari da kuma siyasa a jihar.

Hirar tashi da Buhari kan matsayin tsohon gwamna Yari a karkashin Jam’iyyar APC ya gudana ne kafin zaben takarar gwamna a jihar.

Ko da shike dai Yarima ya lura cewa shugaban kasar a yayin tattaunawarsu ya nuna rashin jituwarsa game da zancen dan takarar, Yari, a wannan lokacin.

Ka tuna da cewa Sanatan da ya wakilci Jihar Kaduna a Majalisar Dattajai na takwas, Sanata Shehu Sani yayi kira da gargadin Arewa su manta da zancen neman shugabancin kasar Najeriya daga Arewacin kasar a zaben shugaban kasa ta 2023 da ke a gaba.

“Ku manta da batun neman wanda zai maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari a shugabancin Najeriya a zaben shugaban kasa ta 2023” inji shi.